Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/06 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/06 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/06 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/06 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/06 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/06 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Turai

May ta dakatar da kuri'ar Majalisa kan shirinta na ficewa daga EU

media Ranar 29 ga watan maris mai zuwa ne ya kamata Birtaniya ta fice baki daya daga gungun kasashen na Turai. Parbul TV/Handout via Reuters

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta sanar da jinkirta kada kuri’a a majalisar dokokin kasar, domin jin matsayin majalisar dangane da yarjejeniyar da ta kulla da kasashen Turai kafin ficewar kasar daga kungiyar.

Firaminista Theresa May ta ce bisa ga tattaunawar da ta yi da magoya baya da ma daidaikun mutane, ta fahimci rashin nasarar da za ta iya fuskanta matukar majalisar ta zauna don kada kuri'a kan batun.

Sai dai firaministar ta Birtaniya, ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da kasashen yankin Turai domin samar da mafita dangane da wannan batu, inda ta ce ta yi magana da wasu daga cikin shugabannin Turai a karshen makon da ya gabata, sannan kuma ta na shirin ganawa da shugabannin wasu kasashen kafin daga bisani ta sake ganawa da shugabannin majalisar Turai.

May ta ce za ta yi kokarin sanar da su damuwar majalisar, duba da muhimmancin da ta ke da shi ga batun ko da dai ta ce akwai wadanda ke fatan ganin an gaggauta rabuwar tsakaninsu da EU.

Theresa May dai na ganin cewa sake shirya sabuwar kuri’ar jin ra’ayin ‘yan Birtaniya kan wannan batu, ba abin da zai haifar face raba kan ‘yan kasar.

Ranar 29 ga watan maris mai zuwa ne ya kamata Birtaniya ta fice baki daya daga gungun kasashen na Turai.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure