Isa ga babban shafi
Amurka

An yi bikin bankwana da gawar tsohon shugaban Amurka

Shugaba Donald Trump da dukkan tsaffin shugabanin Amurka da ke raye da kuma shugabanin kasashen ketare, sun halarci jana’izar bankwana da marigayi George H.W. Bush.

Shugaban Amurka Donald Trump  da uwargidansa Melania yayin bankwana da gawar tsohon shugaban Amurka George H.W Bush. 3/12/2018.
Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania yayin bankwana da gawar tsohon shugaban Amurka George H.W Bush. 3/12/2018. hawn Thew/Pool via REUTERS
Talla

Tsohon shugaban Amurkan na 41 ya mutu ne a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba, yana da shekaru 94 a duniya, wanda ake ganin ya jaogarancin kasar ba tare da nuna wani bangaranci ba.

Jana’izar bankwanar ta samu halartar sarakuna da shugabanin kasashe duniya da dama, da suka hada da Yarima Sharle, da sarkin Jordan Abdallah na 2, sarauniya Raniya sai kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran shugabanni da dama.

An soma bikin ganawar bankwanar tare da shugaba Donald Trump da uwargidansa Melaniya da kuma iyalan marigayi Bush, a cikinsu akwai dansa tsohon shugaban Amurka na 43 George W. Bush.

Marigayin ya shugabanci Amurka daga shekarar 1989 zuwa 1993, wanda ya taka rawa wajen kawo karshen yakin cacar baki tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet, Rasha a Yanzu.

Za kuma a rika tuna gwamnatin tsohon shugaban na Amurka da rawar da ta taka wajen kafa makekiyar rundunar sojin kasar mai karfin dakaru dubu 400,000 da kuma hadakar karin wasu dakarun na kawayenta, domin fatattakar sojojin Iraqi a karkashin gwamnatin marigayi Saddam Hussien da suka mamaye kasar Kuwaiti a waccan lokacin.

An dai haifi Goerge H.W. Bush a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1924, kuma mahaifansa sune Sanata Prescott Bush da Dorothy Bush.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.