Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta dakatar da aniyarta ta karin haraji kan makamashi

Fira Ministan Faransa Édouard Philippe ya sanar da matakin gwamnatin kasar na janye karin da ta yi kan farashin albarkun mai da kuma lantarki.Matakin karin farashin dai, ya janyo kazamar zanga-zangar dubban 'yan kasar, lamarin da ya haifar da arrangama tsakaninsu da jami'an tsaro, musamman a birnin Paris inda aka kone dukiya mai tarin yawa.

Daya daga cikin masu zanga zangar kyamar karin haraji kan makamashi a Paris
Daya daga cikin masu zanga zangar kyamar karin haraji kan makamashi a Paris REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Yayin sanar da janye karin, Fira Minista Edouard Philippe ya ce dakatar da karin zai kasance na tsawon watanni 6, kafin gwamnati ta yanke shawarar aiwatar da shi ko akasin haka, bayan gudanar da muhawara tsakanin wakilan gwamnati da jagororin masu zanga-zangar adawa da karin farashin albarkatun man.

Zuwa yanzu dai mutane uku suka rasa rayukansu, tun bayan da zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma da barnata dukiya, yayinda kuma ‘yan sanda suka kama sama da mutane 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.