Isa ga babban shafi
Faransa-Macron

Macron ya dau aniyar kulle tashoshin nukiliyar Faransa 14

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jaddada matsayin sa kan sauye-sauyen da ya sha alwashin samarwa a kasar duk da fushin masu zanga-zangar adawa da manufofinsa, da suka yi arangama da jami’an tsaron kasar a karshen mako, inda ya ce yana kan bakarsa game da karin harajin man fetur baya ga kulle wasu tashoshin makamashi.

Cikin jawaban na sa Emmanuel Macron ya ce Faransawa ba su zabe shi don ya fice daga yarjejeniyar nukiliya ba face bisa alkawarin rage yawan makamashin nukiliyar da akalla kashi 50.
Cikin jawaban na sa Emmanuel Macron ya ce Faransawa ba su zabe shi don ya fice daga yarjejeniyar nukiliya ba face bisa alkawarin rage yawan makamashin nukiliyar da akalla kashi 50. REUTERS
Talla

Cikin jawaban da ya gabatar yau Talata shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya ce yanzu lokaci ne na kawo shawarwari ba tare da nuna adawa ba.

A cewar sa duk kungiyoyin da ke da bukatar kawo sauyi kai tsaye su na iya ba da shawarwarinsu, masamman wakilan masu zanga-zangar adawa da sauye sauyen a kowane yanki maimakon tunzura mutane su ci gaba da bore.

Macron ya tabbatar da cewa Faransa za ta kulle tashoshin makamashi har 14 na kasar kafin nan da shekarar 2035 karkashin matakan da ya ke dauka na yaki da dumamar yanayi.

Cikin jawaban na sa Emmanuel Macron ya ce Faransawa ba su zabe shi don ya fice daga yarjejeniyar nukiliya ba face bisa alkawarin rage yawan makamashin nukiliyar da akalla kashi 50.

A cewarsa bisa alkawarin da ya ke fatan cikawa al’ummar kasar kamar yadda ya dauka nan da shekarar 2020 zai rufe manyan tashoshin makamashi 2 na Fessenheim, daga bisani kuma a kulle wasu tashoshi 4 zuwa 6 kafin shekara ta 2030 sannan a kammala rufewar a shekara ta 2035.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.