Isa ga babban shafi
Turai-Faransa

Dubban mata na gangamin yaki da cin zarafinsu a Turai

Shekara guda bayan kaddamar da gangamin yaki da cin zarafin mata musamman don kawo karshen yi musu fyade da dukansu dubban mata ne yau din nan a kasashen Turai ciki har da Faransa suka gudanar da wani gangami adawa da cin zarafin mata a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da ranar yaki da cin zarafin matan ta duniya a gobe lahadi.

Matakin na zuwa a dai dai lokacin da ake gab da fara bukukuwan ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya a gobe Lahadi.
Matakin na zuwa a dai dai lokacin da ake gab da fara bukukuwan ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya a gobe Lahadi. Twitter: @nous_toutes
Talla

A Faransa kadai an gudanar da makamancin gangamin a birane 55 ciki har da Marseille da birnin Paris yayinda can a Geneva ma wani dandazon mata ya gudanar da makamancin tattakin.

Tattakin ya samu halartar fitattun mata a Faransa ciki har da jaruma Muriel Robin wadda ta jagoranci mata fiye da dubu guda don gudanar da gangamin.

Wata kididdiga a shekarar 2016 na nuni da cewa akalla mata 123 mazansu ko kuma samarinsu sun hallaka su a Faransa, matakin da ke nuni da cewa ana kashe mace guda duk bayan kwanaki 3 yayinda mata fiye da dubu dari biyu da 20 ke fuskantar cin zarafi daga mazajensu ko tsaffin mazajensu ko kuma a wasu lokutan samarinsu.

Haka zalika wata kididdigar ta daban a shekarar 2017 ta nuna cewa akalla ‘yammata 250 ake yiwa fyade kowacce rana a fadin kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.