Isa ga babban shafi
Faransa

Bikin cika shekaru 100 da kawo karshen Yakin Duniya ya kankama

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na karbar bakuncin shugabannin kasashen akalla 70 a birnin Paris, domin bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1, hadi da karrama tarihin miliyoyin sojin da suka rasa rayukansu a yakin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwararsa ta Jamus Angela Merkel yayin gaisawa da wasu tsaffin sojoji, a wani bangare na bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwararsa ta Jamus Angela Merkel yayin gaisawa da wasu tsaffin sojoji, a wani bangare na bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1. REUTERS/Philippe Wojazer/Pool
Talla

Shugaba Donald Trump na Amurka, Angela Merkel ta Jamus da Vladimir Putin na Rasha, na daga cikin daruruwan manyan bakin da ke halartar bikin, wanda daga bisani za su gana da shugaba Macron a fadar Elysee.

Zalika shugaba Macron zai jagoranci taron zaman lafiya na Paris Peace Forum, wanda zai mayarda hankali wajen tattauna samar da hadin kan kasashe, domin tunkarar matsalolin tsaro da shugabanci, da kuma kaucewa sake tafka kurakuran da suka haifar da barkewar yakin duniya na farko.

Tarihi dai ya nuna cewa da misalin karfe 11 na safiyar ranar 11 ga watan Nuwamba a shekarar 1918, aka kammala kawo karshen yakin duniyar na daya da aka shafe shekaru 4 ana gwabza shi, wanda kuma yayi sanadin hallakar akalla sojoji miliyan 10 da wasu miliyoyin fararen hula.

Yakin duniyar na 1, na daga cikin yake-yake mafiya mafi muni a tarihi, wanda ya taka rawa wajen sauya fasalin siyasar nahiyar Turai.

Sai dai bayan shekaru kusan 20 da kawo karshen yakin duniyar na 1, gwamnatin Nazi ta Jamus a karkashin Adolf Hitler ta yi sanadin barkewar yakin duniya na 2, sakamakon mamaye wasu makwabtanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.