Isa ga babban shafi
Italiya

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 30 a Italiya

Adadin mutanen da suka mutu a Ambaliyar ruwan Tsibirin Sicily na kasar Italiya ya tasamma mutane 30 sabanin 12 da tun farko jami’an agaji suka sanar da safiyar yau.

Tuni dai hukumomi a kasar suka fara gargadin jama'a da su kauracewa yankunan da ake kyautata zaton samun ambaliyar.
Tuni dai hukumomi a kasar suka fara gargadin jama'a da su kauracewa yankunan da ake kyautata zaton samun ambaliyar. Rinsy XIENG / TWITTER / AFP
Talla

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Italiyan, cikin mutane 12 da suka mutu karon farko sanadiyyar ambaliyar ruwan, 9 daga ciki ‘yan gida guda ne ciki har da yaro mai shekara guda.

Yanzu haka dai akwai yankuna 6 na kasar ta Italiya da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan, yayinda hukumomi ke ci gaba da aikin ceto a yankunan da ambaliyar ta tsananta musamammn yankin Palermo wanda ke gab da teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.