Isa ga babban shafi
Jamus

Macron ya yabawa aniyar Merkel ta sauka daga mulki a 2021.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yabawa shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel dangane da bayyana aniyar sauka daga karagar mulki a shekarar 2021.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron bayan wata ganawa a babban birnin Jamus, Berlin. (15/05/2017).
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron bayan wata ganawa a babban birnin Jamus, Berlin. (15/05/2017). REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Yayin ganawa da manema labarai bayan ganawa da Firaministan Habasha Abiy Ahmed, shugaba Macron yace Merkel bata manta da kudirorin kasashen Turai ba, kuma ta jagoranci kasar ta ta hanya mai kyau.

Dangane da barazanar samun masu tsauraran ra’ayi wajen shugabancin Turai da ake fusaknta yanzu haka, Macron yace rashin gudanar da shugabanci na gari da wasu jam’iyyu keyi, shi ke bada kofa ga wadannan jam’iyyu.

Matakin na Merkel ya bada kafar soma muhawara kan wasu jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta CDU da ka iya nasarar maye gurbinta.

Sanarwar Merkel ta zo ne a dai dai lokacin da jam’iyyarta CDU da SPD ke ci gaba da rasa goyon bayan da suke da shi a Jamus, lamarin da yahaifar musu da shan gagarumin kaye a kanan zabukan da aka yi cikin farkon wannan wata a jihar Bavaria.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar CDU da masu sharhi ke ganin za sui ya maye gurbin Merkel sun hada da babban sakataren Jam’iyyar Annegret Kramp-Karrenbauer, wadda ake wa lakabi da “ Karamar Merkel” saboda manufofinsu kusan guda.

Dan takara na 2 a jam’iyyar ta CDU da ake sa ran zai iya darewa shugabancin gwamnatin Jamus, shi ne Minsitan Lafiyar kasar Jens Spahn mai shekaru 38, wanda Merkel ta bashi mukamin domin neman hadin kan masu ra’ayin rikau na jam’iyyar mai mulki, amma hakan bai hana shi ci gaba da sukar manufofin shugabar ba, musamman ma kan batun karbar bakin-haure, da kuma basu damar zama ‘yan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.