Macron ya yi wa Ministocinsa garanbawul
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi garambawul a Majalisar Ministocinsa, in da ya nada shugaban Jam’iyyarsa mai mulki, Christophe Castaner a matsayin sabon Ministan Cikin Gida.
Wallafawa ranar:
Ana kallon garambawul din a matsayin wani yunkurin Macron na karfafa gwamnatinsa bayan wasu tsoffin ministocinsa da suka hada da na Cikin Gida, Gerard Collomb da na Muhalli, Nicolas Hulot sun yi murabus.
Ministan Kudi, Bruno Le Maire da Ministan Harkokin Waje, Jean Yves Le Drien za su ci gaba da rike mukamansu, yayin da a gefe guda aka nada sabbin Ministocin Noma da na Raya Al’adu.
Kimanin mako guda kenan da ake dakon matakin Macron na garambawul a Majalisar Ministocin nasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu