Shugaba Macron ya gana da Shugaban Koriya ta kudu
Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya gana da Shugaban Faransa a fadar Elysee dake birnin Paris, inda Shugabanin biyu suka tattauna dangane da batutuwa da suka shafi Diflomasiya, Cinikaya da kuma rage dumamar yanayi a Duniya.
Wallafawa ranar:
Shugaba Macron ya bayya farin cikinsa kan ziyarar ta Shugaban Koriya ta kudu da kuma jajantawa Faransawa dangane da ambaliyar da ta afka musu.
A cewar Macron Faransa da Korea ta Kudu na bukatar sake duba hanyoyin fasalta tsarin cinikaya da hulda ta kusa da kasashen duniya kamar yadda dokkokin suka tanada.
Zalika Macron y ace za su mayar da hankali wajen sake duba batutuwan da suka shafi sadarwa, da kuma batun yaki da dumamar yanayi a Duniya.
Ziyarar ta Moon Jea-in na zuwa ne bayan ganawa ta musaman da yayi da manyan jami`an gwamnatin Jamus a Hambourg.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu