Isa ga babban shafi
Faransa-Switzerland

UBS ya gurfana a kotun Paris kan badakalar Dala biliyan 10

Bankin UBS mafi girma a Switzerland ya gurfana gaban wata kotu a birnin Paris, bisa zargin da ake masa na hannu cikin wata badakalar boye kudaden haraji sama da Dala biliyan 10 da ya kamata a biya hukumomin Faransa.

Ginin bankin UBS a Switzerland
Ginin bankin UBS a Switzerland REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Sai da aka shafe shekaru akalla shida hukumomin Faransa na bincike kan wannan zargi, wanda daga karshe a shekarar 2017, manyan alkalan kasar suka shigar da karar Bankin na UBS da reshensa da ke Faransa, bisa zargin su da taimaka wa wasu manyan attajiran kasar, wajen kauce wa biyan kudaden haraji masu yawan gaske daga shekarar 2004 zuwa 2012.

Yawan kudaden harajin da ake zargin bankin da taimakawa wajen kin biyan su ya kai Dala biliyan 11 da miliyan 200.

Tuni bankin ya musanta zargin tare da shan alwashin kare kansa daga abin da ya kira kage da neman durkusar da shi da ake yi.

Muddin kotu ta samu bankin na Switzerland da hannu wajen tafka wannan almundahanar, za a tilasta masa biyan tara da yawanta ta kai rabin kudaden harajin da aka ki biya ko kuma a tilasta masa biyan tarar akalla Euro biliyan 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.