Isa ga babban shafi
faransa

Wasu Faransawa sun kaddamar da shirin karbar 'yan cirani

Wasu fitattun mutane 150 a Faransa da suka hada da malaman jami’oi da masu kare hakkin bil'adama sun kaddamar da wani shirin karbar bakin haure da ke shiga kasar, matakin da ya yi hannun riga da manufofin masu kyamar baki a Turai.

Wasu daga bakin haure da ke neman mafaka a Turai
Wasu daga bakin haure da ke neman mafaka a Turai REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Kaddamar da sabon shirin da fitattaun mutanen suka yi na zuwa ne kwana guda bayan wata takaddamar da aka samu wajen samun kasar da za ta karbi wasu baki 58 da kungiyar agajin Faransa ta ceto a teku.

Daftarin shirin da ya samu sanya hannun Annie Ernaux da Patrick Chamoiseau da Yassine Belatter da Guillaume Maurice da Thomas Piketty, ya samu sanya hannu wasu 'yan kasar ta Faransa sama da dubu 3 da suka bayyana goyan bayansu na inganta yadda kasar ke karbar bakin da ke neman mafaka a cikinta.

Daftarin ya ce, wadannan fitattun mutanen da suka hada da malaman jami’oi da masu kare hakkin bil'adama da masu shirin fina-finai sun bukaci bai wa jama’a damar tafiye-tafiye yadda suke so ba tare da sanya wa jama’a shinge ba.

Sanarwar  ta ce, nan da shekaru 10 masu zuwa za a samu karin bakin da ke tafiye- tafiye da kansu da kuma wadanda tashin hankali ko sauyin yanayi za su tilasta musu neman wani matsuguni, saboda haka ya zama wajibi a bude kofofin manyan kasashen duniya domin karbar ire-iren wadannan mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.