Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya

Rashawa ne suka kai harin makami mai guba- Birtaniya

Hukumomin Birtaniya sun zargi jami’an leken asirin Rasha da kai hari da makami mai guba kan tsohon jami’in leken asirin kasar, Sergei Skripal da 'yarsa. Firamistan kasar Theresa May ta bayyana haka a zauren Majalisa, in da tayi shelar kama mutanen biyu da ake zargi da zaran sun bar kasarsu.

Alexander Petrov da Ruslan Boshirov, Rashawan da Birtaniya ke zargi da kai harin makami mai guba a Birtaniya
Alexander Petrov da Ruslan Boshirov, Rashawan da Birtaniya ke zargi da kai harin makami mai guba a Birtaniya Metroplitan Police handout via REUTERS
Talla

May na zuwa ne jim kadan bayan na mataimakin kwamishinan 'yan Sanda, Neil Basu wanda ya yi cikakken bayani kan yadda mutanen biyu daga Rasha suka shiga kasar da wuraren da suka ziyarta da kuma ficewarsu, tare da nuna hotunansu.

May ta ce " dangane da mutanen biyu, kamar yadda masu bincike da 'yan sanda suka sanar a yau, mun karbi izinin kama su daga Kungiyar Kasashen Turai, kuma nan gaba kadan zamu gabatar da umurnin ga 'yan sandan duniya."

"Rasha na ci gaba da kin mika 'yan kasarta domin fuskantar shari’a a kasashen duniya saboda tanadin kundin tsarin mulkinta, amma daga yanzu duk lokacin da daya daga cikin wadannan mutane ya yi tafiya zuwa wajen Rasha, zamu dauki duk wani matakin tsare su, tasa keyar su zuwa Birtaniya da kuma gabatar da su gaban shari’a." In ji May.

Tuni Rasha ta yi watsi da zargin kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajent, Maria Zakharova ke cewa, sunayen mutanen biyu da ake zargi da hotunansu da kafofin yada labarai suka wallafa basu da tasiri.

Zakharova ta bukaci Birtaniya da ta daina zargi a bainar jama’a zuwa bada hadin kai ta hanyar shari’a domin tabbatar da wadanda suka aikata laifin.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne aka kai harin kan Mr. Skripal mai shekaru 66 da 'yarsa Yulia Skripal mai shekaru 33.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.