Isa ga babban shafi
Faransa

Daya daga ministocin gwamnatin Macron ya yi murabus

Ministan Muhallin Faransa, Nicolas Hulot ya sanar da yin murabus daga kujerarsa, in da ya bayyana rashin daukan matakan tinkarar matsalar sauyin yanayi da kuma barazanar da muhalli ke fuskanta a matsayin dalilan ajiye aikinsa.

Ministan Muhalli na Faransa mai murabus, Nicolas Hulot.
Ministan Muhalli na Faransa mai murabus, Nicolas Hulot. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Hulot wanda tsohon mai gabatar da shirin talabijin ne kuma mai rajin kare muhalli ya sanar da matakin ne a yayin zantawa kai tsaye da gidan rediyon Franceinter, amma ya ce, bai sanar da shugaban kasa, Emmanuel Macron ba a hukumance.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna irin farin jinin da Hulot ke da shi a idon Faransawa, yayin da ake kallon murabus dinsa a matsayin wani gagarumin koma-baya ga shugaba Macron.

Tuni mai magana da yawun gwamnatin Faransa, Benjamin Griveaux ya ce, ya yi takaicin murabus din Hulot.

Griveaux ya ce, ya kasa fahimtar dalilan da suka tilasta masa ajiye aikinsa duk da nasarorin da aka samu tare da shi a shekarar farko ta gwamnatin Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.