Isa ga babban shafi
Brazil

Lula na dada samun karbuwa a Brazil duk da yana daure

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva dake daure a gidan yari sama da 10,000, sun yi tattaki zuwa kotun koli domin yi masa rajistar shiga takarar zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Oktoba.

Dubban magoya bayan tsohon shugaban Brazil Inacio Lula da Silva dake daure a gidan yari, a lokacin da suka yi tattaki zuwa kotun koli domin yi masa rajistar shiga takarar zaben shugaban kasar
Dubban magoya bayan tsohon shugaban Brazil Inacio Lula da Silva dake daure a gidan yari, a lokacin da suka yi tattaki zuwa kotun koli domin yi masa rajistar shiga takarar zaben shugaban kasar REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Magoya bayan dauke da jajayen kaya daga Jam’iyyar ma’aikata sun jajirce cewar Lula mai shekaru 72 ne kawai suke bukatar ya jagorance su.

A wasikar da ya aikewa al’ummar kasar, tsohon shugaban ya shaida musu cewar yayi rajistar shiga zaben, kuma yana da yakinin cewar shi zai iya fitar da kasar daga cikin mummunar yanayin da ta samu kan ta.

Ana saran kotun kotun ta yanke hukunci kan takarar ranar 17 ga watan Satumba.

Tun a watan Afrilun da ya gabata kotu ta daure Lula, bisa samunsa da laifukan aikata ba dai dai ba, a lokacin da ya ke shuagabncin kasar daga shekarar 2003 zuwa 2010.

Daga cikin laifukan da ake zargin Lula da aikatawa akwai karbar cin hanci, to sai dai har yanzu sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka yi ya nuna cewa, Lula ke kan gaba wajen samun karbuwa a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Brazil duk da yana daure, inda akalla kashi daya bisa uku na al’ummar kasar ke goyon bayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.