Isa ga babban shafi
Italiya

Jami'an Italiya na aikin ceto mutane a buraguzan gada

Jami’an agajin Italiya na ci gaba da neman wadanda ke da sauran numfashi da suka makale a buraguzan gadar da ta rufta da motoci a birnin Genoa, yayin da aka fara gudanar da bincike kan musabbabin karyewar katafariyar gadar ta Morandi.

Gadar Morandi da ke birnin Gênova na Itália ta rufta da kanana da manyan motoci
Gadar Morandi da ke birnin Gênova na Itália ta rufta da kanana da manyan motoci REUTERS/Stefano Rellandini
Talla

Ministan Cikin Gidan Kasar, Matteo Salivini ya ce, akalla mutane 35 suka rasa rayukansu bayan gomman motoci sun fado daga saman gadar mai nisan mita 45, kimanin takun kafa 148.

Akalla mutane16 sun jikkata, yayin da wasu suka bace da yawansu ka iya kaiwa 12.

Jami’an kashe gobara 250 daga sassan Italiya na cikin wadanda ke aikin neman masu sauran numfashi a ibtila’in, in da suke amfani da karkuna wajen laluben.

Wani jami’in kashe gobara, Emanuel Giffi ya shaida wa AFP cewa, za su ci gaba da aiki ba dare-ba-rana har sai sun ceto mutun na karshe daga cikin mutanen da ibtila’in ya ritsa da su.

Tuni aka kwashe mutane sama da 400 kan fargabar cewa, sauran sassan gadar ka iya ruftawa.

Ibtla’in ya faru ne a dai dai lokacin da ake tafka ruwan sama mai karfin gaske a ranar Talata.

Hukumomin Italiya sun bayyana ballewar gadar a matsayin mafi munin Ibtila’i da kasar ta taba fuskanta a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.