Isa ga babban shafi
Italiya

Adadin mutanen da suka mutu ya karu a Italiya

Gwamnatin Italiya ta dora alhakin karyewar gadar Morandi ta birnin Genoa kan kamfanin da ya yi aikin samar da ita a shekarar 1960, a dai dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu ya karu zuwa 39 ciki har da kananan yara da shekarunsu bai gaza 12 zuwa 13 ba.

Buraguzan gadar Morandi a Genoa dake kasar Italiya
Buraguzan gadar Morandi a Genoa dake kasar Italiya REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Rahotanni sun ce akwai kuma kusan mutane 20 da suka jikkata yayinda wasu da dama suka bace ,hadarin wanda ya faru jiya talata bayan wani ruwan sama mai karfi hade da tsawa wanda aka shafe tsawon lokaci ana tafkawa a yankin arewacin birnin na Genoa.

Yankin dake da yawan tekuna, binciken farko ya baiwa gwamnati damar gano cewa kamfanin Autostrade per I’Italiya wanda shi ke kula da gyaran titunan kasar.keda alhakin wannan hatsari.

Rahotanni sun ce akalla kananan motoci 35 tare da manya ne suka fada titunan jiragen kasa da ke karkashin gadar ta Morandi wadda aka gina a shekarar 1960 ciki har da Faransawa 3 da ‘yan kasar Chile 3 wadanda dukkaninsu ke gudanar da ayyukansu na Diflomasiyya.

Ministan harkokin cikin gida Matteo Salvini ya ce akwai tarin kananan yara da shekarunsu bai gaza 8 zuwa 13 ba wadanda hadarin ya rutsa da su baya ga tarin jama’ar da har yanzu ba a kai gano su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.