Isa ga babban shafi
Faransa

Tauraro na biyu ga rigar yan wasan Faransa

A Faransa, wata daya kenan da kungiyar kwallon kafar kasar ta lashe kofin Duniya na kwallon kafa a gasar cin kofin da ya gudana a Rasha.Tarihi ya nuna cewa a koda yaushe aka samu kungiyar da lashe kofin a kan sanya alama ko karin tauraro a saman rigar yan wasan.

Faransa ta lashe kofin Duniya na kwallon kafa a Rasha
Faransa ta lashe kofin Duniya na kwallon kafa a Rasha REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Faransa da ta lashe kofin a shekara ta 1998 ta samu tauraro na farko, bayan gaggarumar nasara da yan wasan suka yi tareda doke Crotia da ci 4 da 2,an bayyana cewa a daren da Faransa ta samu wannan nasara, akala magoya bayan kungiyar 1500 ne suka yi rijista wajen sayen rigar mai dauke da tauraru biyu a shafin hukumar kwallon kafar kasar ta FFF.

Mujalar le Parisien ta ruwaito cewa akala riguna 30.000 za a fitar da su ranar alhamis zuwa magoya bayan kungiyar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.