Yankin Turai na fama da tsananin zafi
Tsananin zafi da ake fama da shi a wasu yankunan tarrayar Turai ya hadasa mutuwar mutane uku a kasar Spain, yayinda wasu kasashen irin su Faransa suka sanar da daukar matakai da suka dace domin samarwa jama’a wurare na hutu musaman gajiyayu.
Wallafawa ranar:
A kasar Fotugal an bayyana cewa zafi ya fi muni, hukumomin kasar sun gargadi jama’a da su yi taka cantsa, yayinda a Sweden aka soma fuskantar narkewar kankara, a Italiya hukumomin kasar sun soma rabbawa jama’a ruwan sha a kyauta.
Tsawon makwonni uku da suka gabata dai saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu yankuna na Nahiyar Turai ya saukaka tsananin zafin da ake fuskanta sakamakon gobarar dajin girka da ta hallaka mutane 82 tare da jikkata da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu