Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai gana da May gobe a birnin Paris

Fadar Shugaban Faransa ta ce ganawar da za’ayi gobe tsakanin shugaba Emmanuel Macron da Firaministan Birtanya Theresa May za ta mayar da hankali ne kan tattaunawar ficewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai.

Sanarwar ta ce babu jawabin da za’a yi wa manema labarai bayan ganawar ta Macron da May.
Sanarwar ta ce babu jawabin da za’a yi wa manema labarai bayan ganawar ta Macron da May. Reuters/路透社
Talla

Sanarwar da fadar ta bayar ya nuna cewar da tsakar ranar gobe ne shugaba Emmanuel Macron zai tarbi Firaminista Theresa May a katafariyar fadar shugaban kasar da ke gabar ruwan Begancon, inda zai fara hutu daga yau.

Sanarwar ta ce shugabannin biyu za su gudanar da taron sa’oi biyu, daga nan kuma za su hadu da matar shugaba Macron Brigitte da mijin Theresa May, Philip inda za su ci abinci su hudu a farfajiyar da za su dinga kallon tekun meditereniya.

Fadar shugaban ta ce taron na su zai bai wa Theresa May wadda ke dawowa daga hutun da ta tafi a Italia damar yi wa shugaba Macron bayani kan matsayin Birtaniya dangane da tattaunawar ficewar kasar daga kungiyar Turai.

Sanarwar ta ce babu jawabin da za’a yiwa manema labarai bayan ganawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.