Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

Rashin cimma matsayar Birtaniya da EU babban kalubale ne - Hunt

Ministan harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya yi gargadin hadurran da kasar ke iya fuskanta a dai dai lokacin da ta ke kokarin raba gari da takwarorinta na EU ba kuma tare da cimma wata matsaya kan shirin ficewarta daga kungiyar ba.Yayin tattaunawarsa da takwaransa ministar harkokin wajen Austria Karin Kneissl, Mr Hunt ya ce Birtaniyar na tunkarar mafi munin kuskure a tarihi.

Firaministar Birtaniya Theresa May.
Firaministar Birtaniya Theresa May. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Mr Jeremy Hunt wanda ke ziyarar aiki a Austria, ya ce Birtaniya ba ta kai ga cimma yarjeniyoyin da suka kamata da kasashen kungiyar ta EU ba, wanda ke nuna cewa ta na tunkarar ficewar ne ba tare da wani shiri a kasa ba.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala ganawa da takwaransa na Austria, Mr Hunt ya ce rashin kammala tattaunawa kan ficewar ta Birtaniyar da kungiyar EU zai cutar da hatta al’ummar kasar.

Ministan harkokin wajen na Austria, Karin Kneissl ya ce bisa ga ka’idojin da kungiyar ta EU ta gindaya kan birtaniyar game da ficewarta, a fili ya ke cewa ta gamsu da batun.

Ziyarar ta Mr Hunt wadda ke zuwa kwana guda bayan kai makamanciyarta Faransa duk dai a yunkurin ganin kungiyar ta EU ta mutunta bukatun Birtaniyar gabanin ficewarta daga kungiyar tarayyar Turan.

Birtaniyar dai na fatan ci gaba da cin gajiyar wasu daga cikin alfanun kungiyar ko da bayan ficewarta da wasu lokuta, ciki kuwa hadda tallafin noma dana cinikayya tsakaninta da kasashen na EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.