Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta zaftare kasafin kudin kafafen yada labarai

Gwamnatin Faransa na shirin zaftare Euro milyan 190 daga cikin kudaden da take ware wa kafafen yada labarai mallakin gwamnati, wannan kuwa domin yin tsimin kudi kamar yadda Emmanuel Macron ya alkawarta.

A cikin watan yunin da ya gabata ne gwamnati ta sanar da shirinta na aiwatar da sauye-sauye a kafafen yada labaran
A cikin watan yunin da ya gabata ne gwamnati ta sanar da shirinta na aiwatar da sauye-sauye a kafafen yada labaran REUTERS/Gonzalo Fuentes/Pool
Talla

Wannan dai shiri ne da zai fara aiki daga shekara ta 2019, inda sannun a hankali za a zaftare Euro milyan 160 kafin karshen shekara ta 2022.

Radio France da ke watsa shirye-shiryensa a cikin gida, zai wayi gari an rage kudadensa Euro milyan 20, yayin da sauraren kafafe da suka hada da Arte, TV5Monde, France Médias Monde, wadda a karkashinta ne France 24 da kuma RFI ke yada shirye-shiryensu za su rasa Euro milyan 10.

A cikin watan yunin da ya gabata ne gwamnati ta sanar da shirinta na aiwatar da sauye-sauye a kafafen yada labaran, to sai dai a lokacin ba a bayyana adadin kudaden da shirin zai shafa ba.

A jimilce dai, gwamnatin Faransa za ta kashe Euro Bilyan 3 da milyan 800 domin daukar dawainiyar kafafen yada labaranta na ciki da kuma na ketare a wannan shekara, to sai dai sakamakon matsin tattalin arziki, kasar za ta rage kudaden tare da rufe wasu gidajen talabijin a cewar sanarwar da aka fitar a wannan alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.