Isa ga babban shafi
Jamus-Bakin haure

Merkel ta yi nasarar ceto gwamnatinta daga rugujewa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi nasarar ceto gwamnatinta daga rugujewa ta hanyar cimma matsaya da shugaban jam’iyyar masu ra’ayin rikau kuma ministan cikin gidan kasar Horst Seehofer kan yadda ya kamata Jamus ta tunkari matsalar ‘yan ci rani.

shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ministan harkokin cikin gida Horst Seehofer bayan kammala cimma matsaya game da tarnaki da ya taso kan kwararowar 'yancirani.
shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ministan harkokin cikin gida Horst Seehofer bayan kammala cimma matsaya game da tarnaki da ya taso kan kwararowar 'yancirani. REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Bangarorin biyu sun amince da kafa wani sansanin tantance wadanda ke neman shiga Jamus a kusa da iyakar kasar da Austria, abin da ya kawo karshen barazanar da ministan cikin gidan ya yi na marabus daga mukaminsa matukar dai kasar ba ta dauki mataki kan wannan batu ba.

An jima dai ana fuskantar takun saka tsakanin Merkel da ministan na ta wanda ke ganin kwararowar bakin haure kasar shi ke kara yawan ayyukan ta'addanci da rashoin aikin yi a kasar.

Bayan kammala cimma matsaya kan batun, an hango shugaba Angela Merkel na musafaha da Minista Host Seehofer wanda a baya ya yi barazanar ficewa daga gwamnatin kawancen ta Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.