Isa ga babban shafi
Faransa-kwadago

Majalisar Faransa ta amince da kudirin Macron kan kamfanin jiragen kasa

Wakilan Majalisar Faransa sun zartas da doka kan sabbin sauye-sauyen da ya shafi jiragen kasa wanda shugaba Emmanuel Macron ya gabatar masu da ya haifar da rashin jituwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Zartas da wannan sabuwar doka da wakilan majalisar Faransa suka yi dai, za ta kasance ta karya lagon kungiyoyin kodagon da ke Faransa, wadanda suka kwashe watanni 3 suna yajin aiki don adawa da wannan doka, yayin aikin da ake ganin ita tafi tsawo a fannin jiragen kasa, cikin shekaru 30 da suka gabata.

Wakilan karamar Majalisar Faransa inda jam'iyyar Shugaba Macron ke da rinjaye sun amince da dokar da kuriu 425 yayinda wakilai 80 ke adawa da dokar.

Masu sharhi kan siyasa a Turai na kwatanta rashin jituwa tsakanin ma'aikatar jiragen kasan da Shugaba Macron da abinda ya faru a Britania cikin shekarar 1980 tsakanin Margrate Thatcher da masu hakar ma'adinai na Britania.

Ma'aikatan jiragen kasa na Faransa su na adawa ne da dukkan matakan da zai kai ga rage ma'aikata, da ganin ba’a taba masu kudaden Fansho ba.

Gwamnatin Faransa na cewa shi kamfanin jiragen kasan kasar na fama ne da dimbin basuka, da ya zama dole a rage wasu nauyi da ke wuyansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.