Isa ga babban shafi
Iran-Turai

Kasashen Turai 3 sun roki Amurka don ceto kamfanoninsu a Iran

A wata wasikar hadin gwiwa da ministocin kudi da na harakokin wajen Kasashen Faransa, Jamus da Britaniya suka sanyawa hannu sun roki Amurka, kan ta tsame kamfanoninsu daga cikin sabin takunkuman da ta sakawa kamfanonin da ke ci gaba da aiki a Iran.

Kasashen na Faransa Jamus da kuma Birtaniya na fatar ganin sabbin takunkuman na ta kan Iran ka da su shafi kamfanonin da alúmmar turai.
Kasashen na Faransa Jamus da kuma Birtaniya na fatar ganin sabbin takunkuman na ta kan Iran ka da su shafi kamfanonin da alúmmar turai. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Wasikar mai dauke da kwanan 4 ga wannan watan nan na Yuni, ga Sakataren wajen na Amurka Mike Pompeo da na baitilmali Steven Mnuchin, wadda ministan kudin Faransa Bruno Le Maireya ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta nuna yadda ma'aikatun kudi dana harkokin wajen kasashen 3 ke neman Amurka ta dakatar da daukar mataki kan kamfanoninsu baya da suka ki amincewa da matakinta na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

A cewar Fransa Jamus da kuma Britaniya akwai bukatar Amurkan ta dakatar da daukar duk wani mataki da zai haifar da tarnaki ga muradu da kuma tsaron nahiyar Turai.

A cikin wasikar ta hadin guiwa da ta samu saka hannun Shugabar ofishin kare manufofin ketare ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, ta ce ko da kasar Amurka ta yanke hukuncin ficewa daga cikin yarjejeniyar nukliyar Iran, su a kullum sun yi amanar cewa yarjejeniyar ce hanya mafi dacewa wajen hana kasar Iran mallakar makaman Nukliya.

Moghereni ta ce a matsayinsu na kawaye ga Amurka su na fatar ganin sabbin takunkuman na ta kan Iran ka da su shafi kamfanonin da alúmmar turai.

Har ila yau kasashen 3 na fatan ganin Amruka ta mutunta matsayin siyasar da suka dauka, haka kuma daukacin yan kasuwa da yan kwangilar halataciyar nahiyar ta turai, na rokon ganin Amruka ta janye kamfanoninsu da suka fara aiki a kasar ta Iran daga cikin takunkuman, domin samun damar kammala kwangilolin da suka kulla da kasar Iran tun bayan fara aikin da yarjejeniyar nukliyar ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.