Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda ke ziyarar neman goyan bayan kasashen Turai wajen ganin sun yi watsi da yarjejeniyar Iran, bai samu biyan bukata ba daga shugaban Faransa Emmanuel Macron kamar yada shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shaida masa.
Firaminista Netanyahu ya cigaba da zargin Iran a matsayin mai nema jefa gabas ta tsakiya da kuma Turai cikin tashin hankali.