Isa ga babban shafi
EU-US

Angela Markel ta amsa kiran shugaba Macron kan ceto tattalin arzikin Turai

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta fayyace amsar da aka dauki tsawon lokaci ana dako kan bukatar shugaban Faransa Emmanuel Macron game da samar da sauye-sauye a Kungiyar Kasashen Turai, matakin da zai bude kofar cimma jituwa kan zuba hannayen jari tare da taimaka wa mambobin Kungiyar da ke cikin kangin basuka.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel 路透社
Talla

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke hira da jaridar Frankfurter Allgemeine gabanin babban taron kungiyar kasashen Turai a cikin wannan wata ta ce, kasarta wadda ta kasance mafi karfin tattalin arziki a Turai, za ta bada goyon baya kan tsarin kasafin kudin zuba jari da jimillarsa bata zarce wani adadi na biliyoyin kudi ba.

Merkel ta ce, wadannan kudade da ake yi wa lakabi da “kudeden ajiya don amfanin gaba” za su taimaka wajen samar da daidaiton tattalin arzki tsakanin kasashen Turai masu wadata da kuma marasa karfi musamman ta fuskar kimiya da fasaha da kuma kirkire-kirkire.

A cewar Merker, dole ne su karfafa hanyoyin zuba jari don cimma wannan muradi.

Sama da shekara guda kenan da shugaban Faransa Eammunel Macron ya bayyana kudirinsa na karfafa Kungiyar Kasashen Turai don ganin sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kula da al’ummominsu.

Ko da dai hasashen Merkel na zuba jarin ya yi kasa da adadin da shugaba Macron ya bukata, amma amsar da ta bayar tamkar cimma jituwa ne tsakanin ra’ayoyin shugabannin biyu kan cewar, tsattsauran tsarin tsuke bakin aljihu na tauye tagomashin nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.