Isa ga babban shafi

EU ta kaddamar shirin maida wa Amurka martani kan haraji

Kungiyar tarayyar turai ta kaddamar da shirinta kashin farko na maida wa Amurka martani dangane da kakaba biyan haraji kan karafa da aluminium da kasashe manbobinta ke shigarwa Amurkan.

Shugabar sashin huldar kasuwanci ta kungiyar tarayyar turai Cecilia Malmstrom.
Shugabar sashin huldar kasuwanci ta kungiyar tarayyar turai Cecilia Malmstrom. REUTERS/Yves Herman
Talla

Shugabar sashin huldar kasuwanci ta kungiyar Cecilia Malmstrom ta ce EU zata kakaba haraji akan wasu kayayyakin da Amurka ke shigarwa tarayyar turan da darajarsu ta haura dala biliyan 3 ciki harda baburan hawa, da kuma kayan sawa.

Kasar Canada ma ta bi sawu inda ta sanar da kakaba haraji akan kayayyakin da Amurka ke shigar wa cikinta, wadanda darajarsu ta kusan dala biliyan 13, yayin da Mexico ta sanar da shirinta na kakaba nata harajin akan karafa da kayan albarkatun noma da Amurka ke shigar wa kasar.

Wata kididdiga ta nuna cewa a shekarar 2017 kadai, Canada, Mexico da kuma wasu kasashen kungiyar tarayyar turai, sun shigar da karafa da kuma Aluminium da darajar kudinsu ya kai dala biliyan 23, kusan rabin jimillar karafa da aluminium da Amurkan ta saya daga kasashen ketare a shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.