Isa ga babban shafi
Spain

An tsige Firaministan Spain daga mukaminsa kan rashawa

Firaministan Spain Mariano Rajoy ya yi rashin nasara a kuri’ar yankan kauna da majalisar dokokin kasar ta kada akansa yau din nan, bayan bangaren adawa ya shigar da bukatar hakan sakamakon zargin cin hanci da rashawa da ake kan Firaministan.

Rajoy dai shi ne Firaminista na farko a Spain da ya taba yin rashin nasara a kuri’ar yankan kauna.
Rajoy dai shi ne Firaminista na farko a Spain da ya taba yin rashin nasara a kuri’ar yankan kauna. REUTERS
Talla

Tun farko dai Jagoran masu ra’ayin gurguzu Pedro Sanchez ne ya shigar da korafi kan Firaministan inda ya ke neman majalisar ta hukunta shi kan zargin cin hancin.

Gabanin kada kuri’ar yau Juma’a Mr Sanchez ya ce kuri’ar yankan kaunar kan Mariano Rajoy ita za ta bude sabon babi ga Dimokradiyyar kasar ta Spain.

Rajoy dai shi ne Firaminista na farko a Spain da ya taba yin rashin nasara a kuri’ar yankan kauna.

A jawabin da ya gabatar bayan shan kaye a kuri’ar yankan kaunar Mr Rajoy wanda jam’iyyar sa ta PP ke jagorancin Spain tun daga 2011, ya ce abin alfaharinsa ne ganin yadda ya ciyar da kasar gaba sabanin yadda ya karbe ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.