Isa ga babban shafi
Italiya

Sabuwar gwamnatin Italiya zata karbi rantsuwar soma aiki a gobe asabar

An sake zabar Guiseppe Conte a mukamin Firaministan kasar Italiya, wanda ya sanar da yi murabus ranar lahadi da ta gabata ,bayan da shugaban kasar ya nuna adawa dangane da sunayen wasu da aka gabatar masa.

Sergio Mattarella Shugaban Italiya da sabon Firaminita Giuseppe Conte a fadar Gwamnati dake Roma
Sergio Mattarella Shugaban Italiya da sabon Firaminita Giuseppe Conte a fadar Gwamnati dake Roma Italian Presidential Press Office/Reuters
Talla

Kasar Italiya ta share kusan watanni uku ba tareda yan siyasa sun cimma dai-daituwa domin kaffa gwamnati.

Guiseppe Conte dan shekaru 53 masannin dokokin shara’a, Lauya kuma malami a jami’a , ya sake samun amincewar Shugaban kasar domin rike mukamin Firaministan sabuwar gwamnatin kasar Italia da ta kumshi ministoci 18.

Rashin gwamnati a kasar na dan karami lokaci ya janyowa tattalin arzikin kasar koma baya ,wanda yanzu haka sabuwar gwamnatin kasar za ta dukufa domin samun daidato,

Guiseppe Conta ya bayar da sunan Giovanni Tria, masanni tattalin arziki wanda aka baiwa kujerar Ministan kudin kasar lura da cewa ya na daga cikin masu ra’ayin Italiya ta ci gaba da kasancewa a gungun kasashen Turai.

Bangaren ci gaba da hulda da yankin Turai an nada Paolo Savona mai shekaru 81, sai bangaren diflomasiya Enzo Moavero Milanes wanda aka damkawa kujerar Ministan harakokin wajen kasar da zimar sake dawowwa da tagwamashin kasar a fani diflomasiya da sauren kasashen .

A wannan karo mata biyar ne suka samu shiga majalisar Ministocin kasar Italiya da za ta karbi rantsuwar soma aiki a gobe asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.