Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu ta umarci Faransa ta biya nakasasshe Euro miliyan 6

Kotun Kare Hakkin dan Adam ta Tarayyar Turai, ta umurci gwamnatin Faransa ta biya diyyar Euro milyan 6 da dubu 500 ga wani mai suna Abdelkader Ghedir, bayan da ya samu nakasa a hannun jami’an ‘yan sandan kasar a shekarar 2004.

Abdelkader Ghedir, lokacin da yake kwance a asbiti bayan dukan da ya sha a hannun 'yan sandan Faransa
Abdelkader Ghedir, lokacin da yake kwance a asbiti bayan dukan da ya sha a hannun 'yan sandan Faransa twitter.com/ajplusfrancais
Talla

Jami’an tsaro sun cafke Abdelkader ne a ranar 30 ga watan Nuwambar 2004 a wata tashar jirgin Mitry-mory da ke Paris, bisa zargin cewa ya jefa dutse akan wani jirgin kasa da ke wucewa.

Bayanai na cewa, bayan jami’an tsaron tashar jirgin sun mika shi ga ‘yan sanda, Abdelkader ya sha dukan tsiya tare da daure hannayensa na wani lokaci, abin da ya haddasa ma sa nakasar a kusan kashi 90 cikin 100 na sassan jikinsa.

Kazalika an kwantar da shi a asibiti bayan ya fita hayyacinsa sakamakon azabar da ya sha a hannun ‘yan sandan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.