Ana zargin tsohon minista da karbo kudin yakin neman zabe daga Libya
Kotu ta fara binciken tsohon minista a gwamnatin Nicolas Sarkozy na Faransa, bisa zargin hannu wajen karbo kudaden yakin neman zaben tsohon shugaban kasar a 2007 daga Libya.
Wallafawa ranar:
Tsohon minista Eric Woerth shi ne babban ma’ajin kudi na kwamitin yakin neman zaben Sarkozy, kuma har yanzu shi ne shugaban Kwamitin Kudade a majalisar dokokin Faransa.
A watan satumbar 2017 ne sashen binciken zargin rashawa na rundunar ‘yan sandan kasar ya fara binciken tsohon ministan, dangane da rawar da ya taka wajen karbo makudden kudade daga tsohon shugaban Libya Mu’ammar Kadhaffi don tallafa wa yakin neman zaben Nicolas Sarkoz a 2007.
Sarkozy da kansa sau da dama yana gurfana a gaban ‘yan sanda da ke binciken zargin, kafin daga bisani a mika shi a hannun alkalai domin tuhuma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu