Faransa za ta fice daga matsalar gibin kasafin kudi
Kungiyar Tarayyar Turai ta tsayar da shawarar janye Faransa daga cikin jerin kasashen da ke fama da matsalar gibin kasafin kudi a Turai. Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta shafe sama da shekaru 10 ta na fama da matsalar.
Wallafawa ranar:
Ana ganin shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya tsaya kai da fata don samun amincewa daga Jamus wadda ke hankoron ganin an kakaba wa Faransa dokar tsuke bakin aljihu.
Hukumaar Tarayyar Turai ta bukaci a janye Faransa daga tsarin matsanancin gibin kudaden wanda aka fara kaddamarwa a shekarar 2009, lokacin da kasashen da ke amfani da takardar kudi na Euro suka tsindima cikin tarin basuka.
Kwamishinan Harkokin Tattalin Arzikin Tarayyar Turai, Pierre Moscovici ya shaida wa manema labarai cewa, wannan wani lokaci ne mai matukar muhimmanci ga Faransa bayan tsawon shekaru 9 tana cikin wahalar tsarin gibin kudi a kasafinta.
Hukumar Tarayyar Turai dai ta yi hasashen cewa, Faransa za ta samu gibin kashi 2.6 a ma’aunin tattalin arzikinta na GDP a bara, adadin da ya yi kasa da kashi 3 cif cif da EU ta kayyade.
Kazalika a bana, EU na da hasashen cewa, Faransan za ta kai kashi 2.3, sannan kuma a badi ta kai kashi 2.8.
Faransa da Spain ne kadai ke ci gaba da fuskantar barazanar amfani da matsanancin tsarin gibin kudaden da ka iya kai wa ga kakaba musu takunkumai da kuma cin su tara daga Kungiyar Tarayyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu