Isa ga babban shafi

Babu abinda zai hana mu mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran - Moghereni

Kungiyar tarayyar Turai ta shaidawa Amurka babu abinda zai hana kasashen kungiyar ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran, duk da takunkuman da Amurkan ke barazanar sake kakaba wa kamfanonin kasashen na Turai akan Iran.

Shugabar kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar tarayyar turai EU, Federica Mogherini.
Shugabar kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar tarayyar turai EU, Federica Mogherini. REUTERS/Eric Vidal
Talla

Shugabar kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar Federica Mogherini ce ta bayyana matsayin na EU bayan cimma matsaya da mambobin kungiyar suka yi.

A ranar Litinin Amurka ta kara aikewa da sakon kashedi ga kassahen Turai mambobin kungiyar ta EU inda ta gargade su da cewa akwai wasu takunkumman karya tattalin arziki da za ta kakaba wa Iran, kuma zasu shafi dukkanin kamfanonin kasashen Turai da basu yanke hulda da ita ba.

Sai dai shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi fatali da gargadin, tare da gorantawa Amurka cewar ita kadai ake ji, domin yanzu sauran kasashen duniya sun daina karbar matakan da take dauka a madadinsu.

Yace yanzu kassahen Duniya sun farga da magagin da kasar Amura ke yi, kuma duk wani jan ido da Amurka za ta yi ba zai sake bawa kowa tsoro ba.

Amurka ta rasa kimarta ne a lokacin da ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, abinda ya fayyacewa kasashen na Turai da Iran cewar Amurka na neman jefasu cikin hasara ne domin kariyar bukatunta.

Yanzu dai Iran ta sa ido don ganin yadda zata kaya tsakanin Amurka da sauran kasashen Turai da baza su taba bari su yi hasarar makudan kudaden da suke samu daga Iran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.