Isa ga babban shafi
Birtaniya

An kamala daurin auren Yarima Harry da amaryarsa Meghan

A yau asabar aka gudanar bikin daurin auren Yarima Harry na Birtaniya da Meghan Markle a Fadar Windsor inda dubban baki daga sassan duniya suka halarta.Fadar Windsor dake da nisan kilomita kusan 30 da birnin London tayi cikar kwari da daruruwan baki da kuma mutanen gari da suka yi dafifi a titunan da ma’auaranta biyu suka kewaya a keken doki.

Yarima Harry da amaryarsa Meghan a Cocin dake fadar Windsor
Yarima Harry da amaryarsa Meghan a Cocin dake fadar Windsor Owen Humphreys/Pool / REUTERS
Talla

Shugaban mabiya darikar Anglican Justin Welby ya jagoranci bikin daurin auren, yayin da kakan Yarima Harry ya tsaya a madadin mahaifin Meghan saboda rashin halartar sa wajen bikin, sakamakon aikin da aka masa.

Cikin wadanda suka halarci bikin harda Sarauniya Elizabeth ta biyu, yayin da Firaministar kasar Theresa May da shugabannin kasashen duniya suka aike da sakon taya murna da fatan alheri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.