Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu a Faransa za ta ci gaba da sauraron karar Sarkozy a Satumba

Kotun Daukaka kara a Faransa ta bayyana cewar a watan Satumba za ta yanke hukunci ko za’a cigaba da gurfanar da tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy kan tuhumar da ake masa na karbar kudaden yakin neman zaben shekarar 2012 ko kuma a’a.

Kotun ta ce a watan Satumbar ne za ta tsayar da ko za  aci gaba da sauraron karar ta Sarkozy ko akasin haka.
Kotun ta ce a watan Satumbar ne za ta tsayar da ko za aci gaba da sauraron karar ta Sarkozy ko akasin haka. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Kotun ta bayyana haka ne bayan ta kamala sauraron lauyoyin Sarkozy da ke bukatar ganin taki amincewa da bukatar wanda zata masa suna a bainar jama’a da kuma sanya shi zama gidan yari na akalla shekara guda.

Masu gabatar da kara sun ce Sarkozy ya kashe kusan euro miliyan 43 wajen yakin neman zaben sa, wanda ya kusan ribanya abinda doka ta tanada da kuma bada bayanan karya.

Tsohon shugaban yaki amincewa da tuhumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.