Isa ga babban shafi
Wasanni

Madrid ta gaza biyawa Ronaldo tarar da Spain ta sa masa

Fitaccen dan wasan Real Madrid kuma zakaran kwallon duniya da ya lashe kyautar Ballon d’Or a bara Cristiano Ronaldo, ya bukaci Club din sa ya taimaka ya biya masa tarar da Ofishin haraji na Spain ya kakaba masa.

Kusan dai za a iya cewa fitattun 'yan wasan  biyu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun yi kaurin suna wajen kauracewa biyan haraji.
Kusan dai za a iya cewa fitattun 'yan wasan biyu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun yi kaurin suna wajen kauracewa biyan haraji. google.com
Talla

A bara ne dai Spain din ta yi ikirarin cewa Ronaldon dan Portugal mai shekaru 33 ya damfareta ta hanyar kin biyanta wasu kudaden haraji da yawansu ya kai dala miliyan 13, ta hanyar hada baki da wani kamfani wanda ke boye yawan kuadden da ya ke samu.

Matukar dai Ronaldon baya fatan zaman gidan kaso to fa dole ne ya biya gwamnatin Spain din Yuro miliyan 30 wanda kuma tun tuni Ronaldon ke neman Real Madrid ta biya masa amma ta yi kememe da batun.

Yanzu haka dai Ronaldon wanda ke matsayin na biyu a daukar kudi a fagen tamaula bayan takwarinsa na Barcelona Lionel Messi, yana daukar dala dubu 340 kowanne mako.

Ko a bara ma dai sai da fitaccen dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Argentina ya yi ta shiga kotu sakamakon kaucewa biyan haraji ga gwamnatin ta Spain wadda ta ce ya hada baki da mahaifinsa wajen kaucewa biyan harajin ko da ya ke Messin ya ce ba da saninsa ba ne domin yana cike takardu da yawa matakin kenan da ke hana shi karantawa don fahimtar takamaimain abin da ke cikinsu.

Spain din dai ta yankewa Messin hukuncin daurin kusan shekaru 2 a gidan kaso yayinda ta yankewa mahaifinsa hukuncin watanni 15 ko da dai an sauya hukuncin zuwa tara daga bisani.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.