Isa ga babban shafi
Rasha

Majalisar Rasha ta amince da Medvedev a matsayin Firaminista

Majalisar Wakilan Rasha ta kada kuri’ar amincewa da Dmitry Medvedev a matsayin sabon Firaministan Rasha wanda ke a matsayin babban abokin shugaba Vladimir Putin wanda ya lashe zaben kasar a karo na 3.

Shugaban Rasha  Vladimir Putin da Firaministan kasar Dmitry Medvedev
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Firaministan kasar Dmitry Medvedev Sputnik/Ekaterina Shtukina/Pool via REUTERS
Talla

Cikin wasu bayanai da ya gabatar gabanin kada kuri’ar, Medvedev wanda ya shugabanci kasar daga shekarar 2008 zuwa 2012 ya ce, a shirye yake ya yi kowanne irin aiki don ciyar da kasar gaba.

Zaman kada kuri’ar dai ya samu halartar hatta shugaba Vladimir Putin, in da akalla ‘yan majalisu 374 ne suka amince da Medvedev ya sake hawa kujerar ta Firaminista, yayin da wasu 56 suka ki amincewa.

Putin dai ya rike mukamin Firaminista a lokacin Medvedev na matsayin shugaban kasa, in da shi ma Putin din yamzu ya nada shi Firaminsta bayan ya zama shugaban kasar ta Rasha.

Gabanin kada kuri’ar ga Medvedev, Vladimir Putin ya bayyana shi a matsayin jajirtacce wanda ya ce baya bukatar wata sabuwar gabatarwa la’akari da irin hidimar da ya yi wa Rashan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.