Isa ga babban shafi
Armenia

Armenia: Masu zanga-zanga sun datse manyan hanyoyi

Dubban ‘yan kasar Armenia sun amsa kiran jagoran ‘yan adawar kasar Nikol Pashinyan, na cewa su kaddamar da gagarumar zanga-zanga da kuma bijirewa gwamnati, bayan shan kayen da yayi a zaben Fira Minista da ya gudana a zauren majalisar kasar.

Masu zanga-zanga a Armenia a lokacin da suke datse manyan hanyoyin babban birnin kasar Yerevan, don amsa kiran jagoran 'yan adawa Nikol Pashinyan na su bijirewa gwamnati.
Masu zanga-zanga a Armenia a lokacin da suke datse manyan hanyoyin babban birnin kasar Yerevan, don amsa kiran jagoran 'yan adawa Nikol Pashinyan na su bijirewa gwamnati. REUTERS/Gleb Garanich
Talla

A halin da ake ciki tuni masu zanga-zangar suka datse wasu muhimman hanyoyin da ke shiga zuwa babban birnin kasar Yerevan, da kuma hanyar da ta tafi zuwa babban filin jiragen sama da ke birnin.

A ranar Talata ne dai aka mika sunan Nikol Pashinyan mai shekaru 42, wanda tsohon dan jarida ne a matsayin dan takarar Fira Ministan kasar daya tilo a gaban zauren majalisar kasar ta Australia.

Sai dai jam’iyyar Republican ta tsohon Fira minister Sarksyan mai rinjaye a majalisar ta ki goyon bayan jagoran ‘yan adawar, lamarin da wasu masu sharhi ke dangantawa da irin rawar da Pashinyan ya taba takawa a rikicin siyasar kasar.

A zaben shugaban kasar na shekarar 2008 ne dai Nikol Pashinyan ya haddasa wata kazamar tarzoma a Australia saboda rashin amincewa da sakamakon zaben, abinda yasa aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 2.

An dai shafe tsawon kwanaki magoya bayan Pahinyan suna gudanar da zanga-zanga a sassan Australia, wadanda ke nuna kin jinin gwamnati, zanga-zangar da ta tilastawa Fira Ministan kasar Serzh Sarksyan yin murabus a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.