Isa ga babban shafi

Macron ya bukaci Trump ya mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Amurka da ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Amurka Donald Trump.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Amurka Donald Trump. reuters /Kevin Lamarque
Talla

Macron ya bayyana haka ne, yayin jawabin da ya gabatar, bayan isarsa birnin Washington DC a ranar Laraba, yayin da shugaban ke ci gaba da ziyararsa ta kwanaki uku da yake yi a Amurka.

Duk da cewa batun nukiliyar Iran na daga cikin muhimman makasudin ziyarar, shugaban na Faransa ya bayyana shakku akan yiwuwar Trump ya kyale Amurka cikin wannan yarjejeniya, idan aka yi la’akari da manufar Trump ta fifita bukatun Amurka fiye da komai.

Tuni dai Emmanuel Macron ya gabatarwa Trump, daftarin sake fasalta yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, inda a nan gaba zata takaita shirin kasar na kera manyan makamai masu linzami, da kuma karfin fada aji da ta ke da shi ta fuskar soji a yankin gabas ta tsakiya.

Kasashen da ke cikin wannan yarjejeniya sun hada da Rasha, Jamus, China, Birtaniya, Amurka, kungiyar tarayyar turai EU da kuma Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.