Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Faransa

Jami’an ‘yan Sandan kwantar da tarzoma a Faransa sun yi arangama da mutanen da ke adawa da gina wata tashar jiragen sama a yammacin birnin Nantes.

Masu zanga-zangar sun tare da wurin da aka shirya gina tashar jiragen saman a Faransa
Masu zanga-zangar sun tare da wurin da aka shirya gina tashar jiragen saman a Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Rahotanni sun ce, akalla ‘yan sanda dubu 2 da 500 aka baza domin fatattakar masu zanga-zangar da suka gina tantuna har suka tare a wurin da aka shirya ginin.

Masu zanga-zangar sun yi amfani da tantan da konannun tayoyi da itatuwa har ma da turaken wutar lantarki don dakile jami’an ‘yan sandan.

Sai dai ‘yan sandan sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar, yayin da ake iya hangen hayaki na tashi sararin samaniya daga wurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.