Isa ga babban shafi
Faransa

Yajin aikin ma'aikantan jigaren kasa a Faransa

Kasar Faransa zata fuskanci rana ta biyu na yajin aikin ma’aikatan jiragen kasa wanda zai shafi zirga zirgar dubban jama’a a fadin kasar.

Tashar jiragen kasa na SNCF dake Lyon na kasar Faransa
Tashar jiragen kasa na SNCF dake Lyon na kasar Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Kamfanin sufurin jiragen kasa na SNCF ya ce daya daga cikin jiragen sa mai tsananin sauri guda 7 na TGV ne da kuma daya daga cikin 5 dake tafiya yankunan kasar za suyi aiki a yau.

Yajin aikin da ma’aikatan jiragen kasa ke jagoranci ya kuma shafi ma’aikatan kamfanin jiragen saman Air France da masu aikin kwashe shara da wasu ma’aikatan samar da makamashi.

Gwamnatin Emmanuel Macron ta ce kamfanin jiragen dake fama tsananin bashi na bukatar sauye sauye musamman ganin yadda kungiyar kasashen Turai ke shirin bude kofar gasar sufurin jiragen kasa nan da shekarar 2020, amma ma’aikatan sun ki amincewa da shirin.

Sama da kashi uku bisa hudu na direbobin jiragen sun shiga yajin aikin na jiya, yayin da Firaminista Edouard Phillipe ya amsa cewar matafiya za su ci gaba da shan wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.