Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na shirin tsindima cikin mummunan yajin aiki

Kasar Faransa na shirin tsindima cikin yajin aikin watanni uku da zai shafi bangaren zirga-zirgar jiragen kasa a dai dai lokacin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta lashi takobin aiwatar da sauye-sauyenta duk da boren ma’aikata.

Yajin aikin zai jefa sama da mutane miliyan hudu cikin mummunan hali
Yajin aikin zai jefa sama da mutane miliyan hudu cikin mummunan hali REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Da yammacin wannan rana ta Litinin ne ma’aikata a kamfanin jiragen kasa na gwamnati wato SNCF ke fara gudanar da yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka gargadi cewa zai jefa kimanin Fasinjojin jiragen kasa miliyan 4.5 cikin mummunan hali.

Manyan jiragen kasa masu tsananin gudu guda bakawai za su dakatar da zirga-zirga a yayin wannan yajin aiki a kamfanin na SNCF, in da aka tanadi daya tal da zai yi aikin jigilar Fasinjoji.

Kazalika uku daga cikin hudu na jiragen kamfanin Eurostar zai yi aikin jigilar Fasinjoji daga Faransa zuwa London da Brussels, in da kuma jiragen Thalys da ke zuwa Belgium da Netherlands za su yi aikinsu kamar yadda aka saba, amma babu wani jirginsa da zai kwashi mutane zuwa Spain da Italiya da kuma Switzerland.

Har ila yau masu kwashe shara da wasu daga cikin ma’aikatan makamashi da kuma kamfanin Air France za su shiga yajin aikin da ake kallo a matsayin mafi girma tun bayan darewar shugaba Macron karagar mulki a cikn watan Mayun bara.

Ana saran kawo karshen yajin aikin a fannin jiragen kasa a ranar 28 ga watan Juni mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.