Isa ga babban shafi
Turai-Gaza

Sojin Isra'ila sun kashe mutane 16 da jikkata sama da 1,400 a Gaza

Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci gudanar da bincike mai zaman kan sa kan amfani da karfin da ya wuce kima da Israila tayi a Gaza, wanda yayi sanadiyar kashe Falasdinawa 16.

Yankin Gaza, da sojin Isra'ila suke kokarin tarwatsa Falesdinawa
Yankin Gaza, da sojin Isra'ila suke kokarin tarwatsa Falesdinawa REUTERS/Amir Cohen
Talla

Shugabar diflomasiyar kungiyar Federico Mogherini ta bayyana cewar kungiyar na alhinin kashe mutanen da akayi, kuma suna jajantawa iyalan su da kuma wadanda hadarin ya ritsa da su.

Jami’ar ta ce yancin fadin albarkacin baki da kuma yancin gangami na daga cikin yancin bil Adama da ya dace kowa ya mutunta.

Ma’aikatar lafiyar Gaza ta tabbatar da cewar Israila ta kashe mutane 16 da jikkata sama da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.