Isa ga babban shafi
Faransa

Jami'in tsaron Faransa ya sadaukar da ransa don ceto rayuka

Wani jami’in dan sandan Faransa Arnaud Beltrame ya zama mutum na hudu da ya rasa ransa sakamakon harin da wani dan bindiga ya kai kan wani katafaren kanti a kudancin Faransa, tare da yin garkuwa da mutane.

Jami'in tsaron Faransa Arnaud Beltrame mai shekaru 45, da ya rasa ransa  sakamakon harin dan bindiga a Kudancin Faransa.
Jami'in tsaron Faransa Arnaud Beltrame mai shekaru 45, da ya rasa ransa sakamakon harin dan bindiga a Kudancin Faransa. AFP
Talla

Beltrame, wanda dan bindigar ya harba tare da caka masa wuka, ya mika kansa ne cikin kantin, domin fansar wata Mata da maharin ya yi garkuwa da ita, kafin daga bisani jami’an tsaro su hallaka dan bindigar.

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Collomb ya ce yabawa dan sanda Beltrame, wanda ya ce ya sadaukar da ransa ga kasarsa Faransa, kuma baza’a manta da bajintarsa ba.

Jimillar mutane 4 dan bindigar mai suna Radouane Lakdim ya hallaka, baya ga jikkata wasu 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.