EU na shirin shiga matakin gaba a ficewar Birtaniya
Shugabannin Tarayyar Turai sun shinfida hanyar shiga zangon gaba na tattaunawar ficewar Birtaniya daga nahiyar, yayin da Firaministar Kasar, Theresa May ta bukaci shugabannin da su yi amfani da sabon-salo a yarjejeniyar ficewar.
Wallafawa ranar:
Shugabannnin Kungiyar Tarayyar Turai 27 da ke taro a birnin Brussels sun amince da sabbin sharuddan yarjejeniyar hulda da Birtaniya bayan ficewarta daga nahiyar.
Mai shiga tsakani a tattaunawar ficewar, Michel Barnier da ya halarci taron na yau, ya ce, sun dauki gamsasshiyar hanyar cimma matsaya game da wannan yarejeniya mai sarkakiya.
Barnier ya kara da cewa, za su fara zaman tattaunawa da gwamnatin Birtaniya game da huldarsu ta bayan ficewa, wadda ya ce dole ne a mutunta sharuddanta da kuma matsayin kungiyar EU har ma da kasuwancin bai-daya.
A cikin watan Mayun shekarar 2019 ne, Birtaniya za ta raba gari da Kungiyar Kasasehen Turai, amma masu shiga tsakani a wannan mako sun amince kan yarjejeniyar ficewar da ta kunshi ci gaba da tattalin zumuncin da ke tsakanin Birtaniya da sauran kasashen na Turai.
Firaministar Birtaniya, da ita ma ta halarci taron na yau a Brussels, ta yi madalla da matsayar da aka cimma, kuma ta ce hakan ya kara bada kwarin gwiwar kammala ficewar baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu