Cikin martinin na Rasha da ake kallo da mafi muni kan matakin Birtaniya, ya sanar da cewa dama Ofishin yada al’adu da ilimi na kasar Britaniya da ke kasarta, ba ya a kan ka’ida don haka daga yau sun kawo karshen aikinsa a kasar.
Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da manyan kasashen yammacin Turai da Amurka ya kara rincabewa ne tun bayan da ita Rashan ta tsunduma hannu a rikice-rikicen kasashen Ukraine da Georgia da ke makwabtaka da ita, kasashen da ke da matukar muhimmanci ga Amruka da Turai ta fannin tsaro, da kuma samun damar kutsa kai a yankunan da Rashan ke makwabata da su, ko da ya ke ita Rashan na kallon batun a matsayin barazanar ga tsaronta.