Isa ga babban shafi
Jamus

An sake dankawa Angela Merkel jan ragamar gwamnatin hadin guiwa

An rantsar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wa’adi na hudu na jagorancin kasar,wa’adi da kuma ake saran ya zama na karshe.Merkel dai ta kafa gwamnatin hadaka ne tsakaninta da wasu jam’iyyun kasar, watanni 6 bayan gudanar da zaben yan majalisar dokoki da jam’iyarta ta CDU ta cimma mummunan koma baya a cikinsa.

uwargida Angela Merkel tare da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, a ranar 14 ga watan Maris 2018 a Berlin.
uwargida Angela Merkel tare da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, a ranar 14 ga watan Maris 2018 a Berlin. REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Merkel ta isa wajen sanye da wata sarka da ke nuna launin Jam’iyyarta tare da rakiyar mai gidanta Joachim Sauer da kuma mahaifiyarta Herlind Kasner mai shekaru 89.

Duk da cewa dai ‘yan majalisu 315 ne kadai daga cikin 365 da suka kada mata kuri’ar amincewa da hadakar ne suka hallarci wajen bikin rantsuwar, amma anga Merkel cike da farin ciki.

Rantsar da shugabar a zagaye na hudun zai wanke bacin ran da ta fuskanta karon farko cikin shekaru 12 da ta shafe tana jagoranci, bayan rashin nasarar ta a zaben watan Satumba da ya haddasa mata koma bayan siyasa.

Ko da ya ke dai har yanzu wasu na ganin babu tabbacin hadakar ta dore har zuwa 2021 kamar yadda ake tsammani, amma dai Merkel ta ce babban abin da za ta sanya a gaba bai wuce gyara kura-kuren da ta ke ganin su suka haddasa mata koma baya a kasar ba.

Haka zalika a bangare guda Merkel, za ta yi kokin tabbatar da wasu sauye-sauye na kai tsaye a kungiyar tarayyar Turai, da za su amfani Jamus, musamman kan al’amuran da suka shafi tsaro, harkokin shige-da fice da kuma manufofin kudi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.