Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi gargadin cin kamfanonin Google da Apple Tara.

Faransa ta gargadi manyan kamfanonin sadarwar Google da Apple kan abinda ta kira yadda suke karya ka’idodin kasuwanci, inda ta yi barazanar dora musu tara mai tsauri.

wata ma amfani da internet wajen gudanar da aikinta
wata ma amfani da internet wajen gudanar da aikinta ®https://www.flickr.com/
Talla

Ministan kudin Faransa, Bruno Le Maire ne ya gabatar da wannan gargadin, inda yake cewa zai gurfanar da kamfanonin Google da Apple a gaban kotun dake kula da harkokin kasuwanci saboda yadda suke taka dokokin kasuwanci a Faransa.

Le Maire yace kamfanonin biyu na Amurka sun sanya haraji akan masu bukatar kafa hanyoyin sadarwa domin samun bayanai, wanda hakan wani laifi ne dake dauke da tarrar euro miliyan biyu da rabi.

Wani bincike da aka gudanar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017 ya bankado yadda kamfanonin biyu ke karya ka’idodin da aka shimfida domin gudanar da ayyukan su a kasar.

Ya zuwa yanzu dai kamfanonin biyu na Amurka sun ki cewa komai kan zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.