Isa ga babban shafi

Tsananin sanyi ya hallaka mutane 60 a Turai

Yawan mutanen da suka hallaka sakamakon matsanancin sanyi a nahiyar turai zuwa yanzu ya kai, 60, kuma a kasar Poland kadai mutane 23 suka hallaka, inda jami’ai suka ce, matakin sanyin ya kai kasa da sifili.

Wani yanki na birnin Rome da dusar kankara mai yawa ta zuba sakamakon tsananin sanyi.
Wani yanki na birnin Rome da dusar kankara mai yawa ta zuba sakamakon tsananin sanyi. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

A kasar Ireland ma tsananin sanyin mai zubar dusar kankara, ya tilasta soke tashin jiragen sama, yayin da da dama daga cikin kasashen turan suke fuskantar makamanciyar matsalar, sakamakon guguwar Emma mai dauki da ruwan sama da dusar kankara, da ke keta yankunan turan.

A kasar Amurka ma akalla mutane 5 suka rasa rayukansu, sakamakon guguwar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Tsananin sanyin ya tilasata dakatar soke sufurin jiragen sama na cikin gida da waje sama da dubu 3000, yayin da ta tilasata dakatar da wasu tashin jiragen akalla dubu 2,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.